Yadda Zaka Duba ko Kayi Nasarar Samun Nirsal Non Interest Load

Barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.

Kamar de yadda kuka sani wannan tallafi na Nirsal non interest loan shiri ne da gwamnati ta shirya bayar da tallafin bashi karkashin bankin nirsal microfinace wanda mutane dayawa suka nema yayin da wasu daga cikin wanda suka nema sun samu wasu kuma har yanzu basu samuba basuma san ina abun ya dosa ba

Amma yanzu zan nuna muku hanyar da zaku bi domin ku duba ko kunyi nasarar samun wannan bashin, sakamakon wasu sim din da sukayi register loan din dashi ya bata wasu kuma ba,ama turo musu sakon yin nasarar samun loan dinba, amma da wannan hanyar zaka iya dubawa kagani ko kayi nasarar samun wannan tallafin bashin na Nirsal load

DAFARKO ZAKASHIGA LINK DIN DA KEKSA DOMIN DUBAWA

https://nibloans.nmfb.com.ng/getofferletter

Idan ka shiga bayan ya bude zai baka wajen da zaka danna domin ka zabi wani bashi ne ka cika a baya, saika duba saika zaba sannan sai kasa Referance Number ka, wato wannan number da ake bayarwa yayin da kazo cika bashin Nirsal din.

Dayan ka gama sakawa saika danna Submit, shikkenan saika dan jira kadan daga nan zai bude maka anan ne zaka gani idan kayi nasarar samu kokuma akasin haka.

Allah ya bada sa’a

Leave a Comment