Yadda zaka mayar da katin waya cikin Account na Bankin Ka
Assalamu alaikum yan uwa ina mana barka da wannan lokaci, to kamar yadda muka saba yau darasin mu zamuyi shine kan yadda mutum zai mayar da katin waya cikin bankin sa.
Domin akwai mutane da dama zakaga mutum yasa katin waya daga bankin sa kuma saiya manta ya saka kudin dayawa a garin saka naira ₦100 sai kaga mutum ya saka naira ₦1000 daya wanda daga karshe mutum zai so ya mayar da wannan dari taran ₦900 cikin bankin sa, sai kuma ya rasa yadda zaiyi toh insha Allah yau nazo mana da hanya mai suki da zamu iya maida katin waya cikin bankin mu kai tsaye.
Akwai hanyoyi da dama da ake maida katin waya zuwa kudi na banki amma mu mun kawo muku wannan hanyar da muke ganin tafi sauki ta hanyar amfani da Application, maimakon muyi amfani da website, duk dama zamu kawo hanyar da zakayi amfani da website din ma anan gaba.
Hanyar da muka kawo itace hanyar amfani da wani Application mai suna Tingtel, wannan Application ana amfani dashi ta hanyoyi da dama ga wasu daga ciki kamar haka:-
(1). Zaka iya sai da katin waya ya koma kudi, itace hanyar da muke magana akai yanzu.
(2). Zaka iya sai da katin waya ta ciki wato Airtime, ko kayiwa mutum VTU ta ciki
A kwai hanyoyi da dama na amfani da wannan Application din, idan kuka daukoshi za kuga duk yadda yake yanada matukar sauki wajen amfani dashi, dan haka kushiga nan inda akasa danna nan sai ku dauko Application din
kaje kasa zakaga Link din
Bayan kun dauko Application din ana bukatar kuyi register ma’ana ku saka bayanan ku idan kukai register shine zai baku damar shiga Application din daganan zaku fahimci har yadda zaku maida katin ku yakoma account din ku batare da shan wahala ba.
Duk abinda mutum bai ganeba idan yadauko Application din yana iya yi mana magana ta comment insha Allah zamu duba mubashi amsa.
Kada amanta wajen yi mana share na duk posting namu da aka karanta domin ‘yan uwa su shigo suma su amfana.
Mungode da kasancewa da azeettv.com
https://play.google.com/store/apps/details?id=tingtel.android
JOIN OUR CHANNEL. Message Graphics Designer on WhatsApp. https://wa.me/message/5POELDQPU5IZJ1